Yadda ake dauko video daga Youtube a saukake

Duba da yadda bukatar dauko bidiyo daga youtube kullum ke kara hauhawa kamar farashin dala a kasuwa, wannan ya sa na ga ya dace na wallafa muku wannan bidiyon wanda zai taimakawa dukkanin masu bukatar dauko bidiyoyi daga youtube.


Maziyarta wannan shafi ina yi muku barka da wannan rana, kuma barka da wannan lokaci, a cikin bidiyon da ke kasa, na yi bayani wara-wara akan wadansu hanyoyi hudu da ake bi wajen dauko bidiyo a youtube.

Kalli cikakken bidiyon:

Baya ga haka, da zarar ka kalli bidiyo za ka fahimci na tattauna akan wadansu sassa masu muhimmanci guda biyu, wadanda suka hadar da yin amfani da applications.

A shawarce zaifi sauki mutum ya yi amfani da applications, tun da daukowa zai yi kawai, in kuma ta website ne ko kuma chrome extension to wannan yana da wahalar sabga.

Amma kuma ta wani sashen yin amfani da chrome extensions da kuma websites ya fi sauki kwarai da gaske.

Da fatan za ku amfana da wannan bidiyon da na dora.

Post a Comment

0 Comments